MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY
Apply now Portal
MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY
  • HOME
  • ABOUT US
    • Meet Us
    • Blog
    • Teaching Staff
    • Non Teaching Staff
    • Gallery
    • Our Alumni
    • Events
  • ADMISSION
    • How To Apply
    • Application Form
  • JOB VACANCY
  • CHECK RESULT
  • CONTACT
Apply now Portal
How to join us

Admission Procedures

MARKAZU RIYADHIL JANNAH

 

Lallai Neman ilmin shari'a yana da matsayi mai girman gaske a Musulunci, domin Allah madaukakin sarki ya yabi ilimi da ma'abutansa yana mai cewa: Ka ce: "Shin, wadanda suka sani da wa?anda ba su sani ba suna daidaita? Ma'abuta hankula kawai suna tunãni." (suratul zumur). Bayan haka:

 

 

   Sabon Tsarin Yin Register:

 Muna da bangarori guda uku, don yin register akai! 

  • Bangaren boarding 
  • Bangaren Alqur'ani online
  • Bangaren Arabiyya online 

Toh ga yadda zaku bi wajen register kai tsaye:

 Form din yana dauke da bangarori guda 3 a yanzu:

1- Bangaren boarding SCHOOL, wanda wannan shashen karatu ne na yara da ake gudanarwa anan Markaz babban Shashe da ke Kaduna. Wanda wannan bayan cikewa online, yana da matakai 3:

(a) Cike form online 

(b) Jiran amincewar hukumar

(c) Sai zuwa harabar makaranta don siyan form, ko ga wanda suke nesa da Kaduna, za su iya samun form din anan wurin mu da ke Kano! 

 

2- Bangaren Arabiyya online: yana da matakai 3:

(a) cike form online da jiran amincewar hukumar Makaranta. 

(b) bayan dalubi ya samu saqon amincewa daga makaranta, ga masu shiga mustawa B, Jim, Dal duk zasu fuskanci interview, don gwada dacewar su ga ajin da suka zabi shiga

(c) bayan kammala interview da samun saqon nasara, sai biyan kudin makaranta da fara karatu

 

Wannan tsarin da muka bijiro da shi, zai inganta abubuwa fiye da na baya, kuma karatu zai fi ?arko da inganci fiye da baya, sannan zamuyi maganin matsala irin:

 

1- Yawan bada uzuri mara amfani

2- Wasa da zuwa duk lokacin da aka ga dama!

3- daukar abinda ake yi bada muhimmanci ba dss

4- cakudewan dalubai da rarrabuwarsu zuwa wasu azuzuwan

 

Wannan matsalolin da makamantan su duk zamuyi maganin su ta wannan tsarin in shaa Allah:

 

Sai dai, tsarin karatu yana nan yadda aka sani:

 

1- Karatu zai kasance TA Telegram ne!

 

2- LIVE da bita zai kasance ta Telegram ko Website din makaranta!

 

3- Attendance wajibi ce dss

Bangaren Alqurani Online da Arabiyya online bayanin su yana ?asa:

1- Danna alamar Signup, ko Apply now domin cike form din makaranta. 

 

2- form din yana dauke da bangarori guda 2, akwai bangaren dalubi, mahaifi/ da mai kulawa

 

3- A cike bayanai da kyau, duk bayanan iri daya ne ga masu son shiga kowane fanni. 

 

4- A tabbatar an cike komai daidai, musamman masu son cikewa yayan su bangaren boarding 

 

5- kudin makaranta da na registration ya bambanta daga na kowanne fanni!. 

 

6- Akwai dokoki da tsare tsaren Makarantar duk zaa gani acikin group din bayan an cike form

 

7- Kowa yana da damar shiga, musamman masu son iya larabci tun daga farko, kuma an so ga mace ta nemi izinin mijinta ko iyayenta kafin kasancewa aciki.

 

1- Biyan kudin makaranta da na form, #5,000 fannin Arabiyya. 

 

2- zaa jira hukumar Makaranta tayi approving! 

 

3- Wajibi ne ga dalubi/daluba su kasance suna da email/gmail wanda yake aiki a wayarsu, don samun saqonni da sanarwa, da samun sakamakon jarabawa da sauransu.

 

4- Wajibi ne dalubi/daluba su kasance suna yin TELEGRAM hade da WHATSAPP, domin dukkan halqat a telegram za'a dinga insha'insu, sanarwa kuma da sauransu a whatsapp.. 

 

5- Wajibi ne ga dalubi/daluba su mallaki littattafan da ake gabatarwa.

 

6- Wajibi ne, dole ne dalubi/daluba su kasance suna bibiyar majmu'a a koda yaushe, in so samu ne su sa ta a zuciyansu, domin bibiya da sa ido a duk karatu ko sanarwa da ake yi..

 

7- Sauraren karatu da yin attendance wannan dole ne ga kowane dalubi/daluba, sauraran kowane karatu ana bada adadin lokaci na iyakarsa, dole dalubai su daure su saurara a iya wannan tsakanin. Kuma amana ne da alqawari akan kowane dalubi ya saurari karatu da kyau tare da fahimta, ko yin tambaya inda ba'a gane ba. Idan dalubi ya kammala saurara sai yayi insha'i a majmu'ar da aka sa karatun ta hanyar reply akan audion. 

 

8- Ana daukan attendance akan dukkan halqat din da aka turo, kuma zaa turo da sunayen wainda suka saurara don su gani a majmu'ar. Sai muyi saving a wurin mu. 

 

8- Yin wajib (aiki, assignment) da ake bayarwa wannan dole ne, wajib ya kasu gida 2, akwai wanda a group za'a tura, akwai wanda individual ne ta private za'a tura.

 

10- Wajibi ne ga kowace daluba ta halarci LIVE da ake gabatarwa a majmu'ar Telegram, akan lokaci, ko don yin karatu, ko bita ko Jarabawa. 

 

11- A kowane karshen zangon karatu bayan kammalawa ana bada sakamakon jarabawa ga wainda suka yi. 

 

12- Duk wanda ya karya mana doka, to zamu cire shi har abada, ko ya fuskanci hukuncin makaranta tare da tara mai karfi ga mai son dawowa. 

 

     Tsarin mu:

 

  • Akwai kudin Biyan Form da Term
  • Telegram da whatsapp
  • Gmail da yin register 
  • Neman izinin magabata
  • Mallakar littattafai
  • Kiyaye sharuddan makaranta
  • Yin wajib.
  • Yin alamun sauraran karatu

 

 

Kar mu manta Manzon Allah (SAW) yana cewa:

 

Wanda Allah ya so ya shiryar dashi da alkhairi sai ya fahimtar dashi addininsa. 

 

 

Management

+2347042745289

+2347069691960

Apply now
MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY Logo

Markazu Riyadil Jannah makaranta ce data shahara wajen karantar da al'umma da Kuma basu tarbiyya ta hanyar online kyauta inda dubban Dalibai suke karatunsu daga sassa daban-daban n...

Company

  • Meet us
  • Blog
  • Teaching Staff
  • Non Teaching Staff
  • Gallery
  • Our alumni
  • Events

Other links

  • Application form
  • Contact us
  • How to apply
  • Login
  • Check result

Contact

  • Kaduna
  • +2348032312988
  • Markazuriyadhiljannah@gmail.com
Download App
App Store Google Play

© 2026 MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY. All rights reserved.