NEMAN TAIMAKON GININ MASALLACI
? MARKAZU RIYADIL JANNAH ?
تعلم فإن العلم أزين للفتى
Neman Taimakon Ginin Masallaci
Markazu Riyadil Jannah Makaranta ce wacce ta Shahara sosai wajen karantar da fannonin ilimi daban - daban a zahiri harma Dana online domin saukakawa Dalibai na Kusa Dana nesa ta yadda dubban dalibai suke samun Damar yin karatu daga sassa daban daban Kuma ba tare da sun biya ko sisi ba.
Sannan Makarantar tana da register da CAC (Gwamnati), Kuma Makaranta ce wacce take da manufofi da tsarurruka Masu matukar kyau domin kawo sauyi Mai kyau a bangaren karantarwa na Addini dama na zamani domin anfanin Musulunci da Musulmi gaba daya.
Daga cikin Manufofin akwai Tsari da Manufa ta Gina...
1-Masallaci na Jumu'a
2-Makarantar Haddar Qur'ani (Tahfeez)
3-University (Jami'a)
4-Asibiti
5-Gidan TV
Da Sauransu
Amma a halin yanxu akwai Ginin Masallaci da Makarantar take son farawa .Alhamdu lillahi a halin yanzu, mun samu filaye plottai goma sha biyar wanda muke ganin zasu ishe mu wannan ayyukan. A KAN HAKA MUKE NEMAN NAIRA MILLION HAMSIN (50,000,000) NA SAYAN FILLIN DA GINI. Don haka ya Kai Dan uwa yake Yar'uwa kada ku bari wannan Dama ta wuce ba tare da Kun Saka naku hannun jarin ba a cikin kasuwancin da babu faduwa a ciki sai Riba.
Allah Yana cewa a cikin Qur'ani:
Wãne ne wanda zai bai wa Allah rance, rance mai kyau, dõmin ribanya masa, ribanyãwa mai yawa? Kuma Allah Shi ne ke damkewa, kuma yana shimfidawa...
مَنْ ذَا الَّذِي يُقْرِضُ اللَّهَ قَرْضًا حَسَنًا فَيُضَاعِفَهُ لَهُ أَضْعَافًا كَثِيرَةً وَاللَّهُ يَقْبِضُ وَيَبْسُطُ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ
Kuma Manzon Allah yace:
Idan mutum ya mutu to dukkanin Ayyukansa sun Tsaya sai Sadaka Mai gudana wacce yayi kafin ya rasu ko ilimi da ya koyar ko Kuma yaro nagari wadda yake masa Addu'a, Muslim ya Rawaito
إِذَا مَاتَ ابنُ آدم انْقَطَعَ عَنْهُ عَمَلُهُ إِلَّا مِنْ ثَلَاثٍ: صَدَقَةٍ جَارِيَةٍ، أو عِلْمٍ يُنْتَفَعُ بِهِ، أَوْ وَلَدٍ صَالِحٍ يَدْعُو لَهُ
Dan haka kada muga girma ko kankantar abinda zamu bada kowa ya bayar da abinda Allah ya hore masa, idan ma bashi dashi ya turawa Wani ko yayi hanyar da wani zai Bada
Mazan Allah yace:
Duk Wanda yayi nuni Zuwa ga Alkhairi to shima Yana da Lada kamar na Wanda ya Aikata, Muslim ya Rawaito
من دلَّ على خير، فله مثلُ أجرِ فاعلِه
AC: NUMBER:1228716746
AC: NAME:MARKAZU RIYADIL-JANNAH ACADEMY LTD
BANK: ZENITH BANK
Haqiqa dukkannin abinda muku bayar Domin Allah to Allah zai maye mana Gurbinsa da wani
قُلْ إِنَّ رَبِّي يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن
يَشَاءُ مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ ۚ وَمَا أَنفَقْتُم مِّن شَيْءٍ فَهُوَ يُخْلِفُهُ ۖ وَهُوَ خَيْرُ الرَّازِقِينَ
Za'a iya tuntubarmu ta Lambobi kamar haka:
+2347042745289
+2347069691960
Kota Email Address din mu:
Markazuriyadiljannah@gmail.com
? Markazu Riyadil Jannah