SABON TSARIN REGISTRATION NA FANNIN ARABIYYA
?MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY?
تعلم فإن العلم أزين للفتى
SABON TSARIN REGISTRATION NA FANNIN ARABIYYA
Manzon Allah sallallahu alayhi wa sallam ya ce: "Duk wanda ya taka wata hanya don neman ilimi, toh Allah zai saukaka masa hanyar shiga Aljanna"
Bayan haka:
Assalamu Alaikum Warahmatulah wabarkatuh, daukacin members, dalubai, da sauran dukkan masu bibiyar shafukan wannan makaranta mai albarka, muna muku fatan alheri.
Wannan makaranta mai albarka, kamar yadda aka sani ta shahara wurin karantarwa a fannoni da dama da suka shafi addini, kuma Alhamdulillahi ficen da ta yi ya huce iya nan, sai ma dai hada yan uwantaka ta musulunci, bada gudunmawa da karfafar mutane.
Alhamdulillahi, ga daluban mu na Fannin Arabiyya, fannin da ake karantar da abinda ya shafi yaren Larabci, Nawhu, sarfu da balaga da sauran su, zasu yi shaida, su bada marki dari bisa dari na yadda Fannin Yake da manyan shirye shirye, sauqaqa karatu, kwarewa wajen koyar da wannan bangarorin, ga wanda farko ne zasu fara, da wanda kuma sun yi nisa, zasu dora ko su gyara, dukka a wannan makaranta sun sami babbar nasara ta koyon Nahwu
A taqaice, bayan kammala dukkan tsare tsare a kowane bangare, da qara samar da lafiyayyen tsarin jadawal na karantarwa, ingancin karatun, kayyadewa dss, wannan makaranta mai albarka ta ga da cewar sauya wasu abubuwa wanda daga ciki akwai tsarin REGISTRATION!
Markaz Riyadhil Jannah Academy, bata da bukatar komai don karantarwa, aa sai dai bisa shawarwari da akayi ta badawa, da kuma irin aikin da ke gaban Markaz wanda dukkan ɗalubai sun san da wannan yasa muka sauke tsarin registration kyauta a wannan fanni, muka dan saka wani abu da zai zama kamar bada gudunmawa ga ayyukan markaz da cigaban ta.
Tsarin Registration zai koma ta Online ne, daga shafin Markaz kai tsaye, imma mutum yana son shiga matakin:
• Boarding ga yara na haddar Alqur'ani
• Haddar Alqur'ani online
• Shiga fannin Arabiyya
Wannan matakai guda 3, ana bukatar cike form da bayanai da yin registration kafin samun gurbin zama, kamar yadda yake..
Tsarin Arabiyya yanzu ya koma, Registration naira dubu biyu #2,000, sai kuma kudin term a wata 3, naira dubu uku kacal! #3,000, a karon farko mutum zai biya jimullar kudi naira dubu biyar #5,000, daga nan kuma, duk term zai biya naira dubu uku #3,000 matsayin kudin term.
Wannan kudi, ba su ne gaban markaz ba, sai dai zaayi duba da la'akari ga wanda suka shirya da gaske karatun zasu yi dss..
Muna fatan zaa karbi wannan sauyi hannu biyu biyu, tare da yiwa markaz addu'a da fatan alheri..
Allah ya karbi ayyukan mu, ya daukaka markaz, ya kaita kololuwar matsayi. Amin
?Daga:
MARKAZ RIYADHIL JANNAH ACADAMY (IDARAH)
01/02/1446
05/08/2024
markazuriyadhiljannah@gmail.com
+234 704 274 5289
+2347069691960